Rikicin Chaina da Amirka kan yankin teku

Rikicin Chaina da Amirka kan yankin teku
Amirka ta yi watsi da ikirarin Chaina na kasancewa mai iko da yankin teku na gabar kudancinta wanda Amirka ke bayyanawa a matsayin yankin ruwan kasa da kasa.

Kasar Amirka ta yi watsi da ikirarin Chaina na 'yancin mallakar yankin tekun kudancin kasar na yankin Pacific. A wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya fitar a ranar Litinin, ya ce wannan yanki da ke tsakanin Tekun Indiya da ta Pacific yankin ruwan kasa da kasa ne, don haka matakin kasar ta Chaina na mallaka wa kanta yankin haramtacce ne.

Mista Pompeo ya tunatar da cewa tun a shekara ta 2016 kotun shari'ar rikicin kasa da kasa da ke a birnin The Hague ta bayyana cewa Chaina ba ta da hurumin mallaka wa kanta wannan yanki, don haka duniya ba za ta taba lamunce wa kasar ta Chaina ta mayar da yankin tekun kudancin nata a karkashin ikonta ba. Sai dai ofishin jakadancin Chaina a Amirka ya ce zargin Amirkar ba shi da tushe.  

News Source:  www.dw.com