Sheikh bin Zayed Al Nahyan ya rasu

Sheikh bin Zayed Al Nahyan ya rasu
An ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki 40, sakamakon rasuwar Sheikh bn Zayed Al-Nahyan na Hadaddiyar Daular Laraba, bayan fama da rashin lafiyar mutuwar barin jiki.

Marigayi bin Zayed Al Nahyan na daga cikin shugabanin da suka farfado da kasar Emirats ta fannin tattalin arziki, da kuma dorata kan turbar kasancewa kasa mai martaba a idon duniya, inda take samun tururuwa daga 'yan kasashen ketare.

Mai shekaru 74 a duniya Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rike manyan mukamai a kasar kan ya dare kan madafan iko a shekarar 2004, bayan da ya gaji mahaifinsa Sheikh Zayed bin Sultan Al Nahyan da ya assasa kasar Dubai.

Marigayin ya rage fita a bainar jama'a tun a cikin watan Janairun 2014, bayan da ya kamu da rashin lafiya ta ciwon mutuwar rabin jiki. An ware zaman makomi na tsawon kwanaki 40 a daukacin fadin kasar don juyayin mutuwar, wacce yanzu haka ta girgiza kasashe da dama na yankin.

News Source:  DW (dw.com)