Shugabannin duniya sun soki harin Faransa

Shugabannin duniya sun soki harin Faransa
Shugabannin kasashen duniya sun yi Allah wadai da harin da aka kai da wuka a birnin Nice na kasar Faransa wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku. Masu bincike a Faransa na daukar harin a matsayin na ta'addanci.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ta kadu matuka da harin ta kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasu. A nata bangaren shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Layen itama ta yi Allah wadai da harin wanda ta ce babu imani a cikinsa.

Firaministan Italiya Giuseppe Conte yace harin ba zai kassara kudirinsu na kare yancin fadin albarkacin baki da wanzar da zaman lafiya ba. Shima da yake tsokaci Firaministan Spain Pedro Sanchez yace tarayyar turai kan su a hade yake wajen adawa da nuna kiyayya kuma za su cigaba da kare yanci da akidun dimukuradiyya da kuma tsaron yan kasa.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter yace mummunan labarin harin da aka kai a mujami'ar Notre-Dame ya girgiza shi matuka. Shugabannin Turan na gudanar da taro ta kafar bidiyo domin nazarin halin da ake ciki.
 

News Source:  DW (dw.com)