Shugabar Bolivia ta kamu da Covid 19

Shugabar Bolivia ta kamu da Covid 19
Shugabar kasar Bolivia ta wucin gadi Jeanine Anez ita ce ta baya-bayan nan a cikin jerin shuwagabannin kasashen duniya da suka kamu da cutar ta Covid 19.

Shugabar ta yanke shawarar daukar gwajin cutar ne bayan da aka sami wasu na kusa da ita a gwamnati da suka kamu da cutar.A farkon wannan satin ne shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya sanar da harbuwa da cutar baya ga firaiministan Birtaniya Boris Johnson wanda shi ma cutar ta taba.  Ya zuwa yanzu dai wannan cuta ta Covid 19 tun bayan bullarta daga kasar China a kaarshen shekarar da ta gabata ta lakume rayukan sama da mutum dubu dari biyar da hamsin yayin da ta harbi wasu sama da miliyan goma sha biyu sai da wadanda suka warke ras daga cutar sun haura miliyan 7 wanda ke nuni da wadanda suka warken sun fi masu mutuwa a sabili da ita wannan cuta da ta zame wa duniya karfen kafa.
 

News Source:  www.dw.com