Sojoji sun killace gidan babban alkali

Sojoji sun killace gidan babban alkali
Sojojin Tunisiya sun killace gidan wani babban alkali don sa ido a kan shiga tare da hana shi fita. An dade ana zargin Bechir Akremi da yin mu'amala da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar.

A kasar Tunisiya mai fama da rikicin shugabanci, sojoji sun killace gidan wani babban alkali don sa ido a kan shiga tare da hana shi fita. Gidan rediyon gwamnatin kasar ya yada labarin killacewa da sojojin suka yi ma fitaccen alkali Bechir Akremi, inda suka ce zai kasance a wannan yanayin har tsawon kwanaki 40 daga wannan Asabar. 

Akremi shi ne mutumin da Kungiyar Human Rights reshen kasar, ke zargi da alaka da wasu kungiyoyin 'yan ta'adda, ana kuma zargin sa da boye wasu muhinman takardu na wadannan 'yan ta'addan.

Yanzu haka, kasar Tunisiya ta shiga wani wani hali na rashin tabbas, bayan sanar da tunbuke firaiministan kasar da kuma jingine aikin majalisar dokoki, da shugaban kasar ya yi, matakin da ya janyo rarrubwar kai tsakanin 'yan kasar masu goyan bayansa da masu adawa da shi.

News Source:  DW (dw.com)