Sudan ta zargi Habasha da kashe sojojinta

Sudan ta zargi Habasha da kashe sojojinta
Dakarun kasar Sudan suna tuhumar sojojin Habasha da kashe jami'an tsaronsu guda bakwai da farar hula daya, wadan da aka kashe suna cikin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar na cewa, tana zargin sojojin Habasha da nuna gawar wadan da suka kashe a bainar jama'a, sanarwar ta kara da cewa akwai ramuwar gayya.

Kawo yanzu babu wani martani daga hukumomin kasar Habasha kan ikirari na sojojin Sudan, a baya-bayan nan ana samun takun saka tsakanin kasashen biyu saboda tashe-tashen hankula a arewacin yankin Tigray na kasar Habasha da kuma yunkiirin Habashar na gina madatsar ruwa a kogin Nilu.

Dubun dubatar 'yan gudun hijira sun tsere zuwa gabashin kasar Sudan bayn barkewar rikicin kabilanci, kuma an yi artabu da sojoji a wani yanki na gonaki da ake rikici a kan iyakar kashen guda biyu.

News Source:  DW (dw.com)