Sulhu tsakanin Armeniya da Azerbaijan

Sulhu tsakanin Armeniya da Azerbaijan
Gwamnatocin kasashen Armeniya da Azerbaijan sun tabbatar da aiki da yarejejeniyar tsagaita wuta da Rasha ta taimaka aka kulla tare da nuna fata kan daurewar zaman lafiyar bayan yaki da aka kwabza.

Firaminista Nikol Pashinyan na kasar Armeniya ya bayyana cewa suna aiwatar da yarejeniyar tsagaita wuta domin kaow karshen rikicin yankin Nagorno-Karabakh da kasar Azerbaijan karkashin shirin zaman lafiya da Rasha ta taimaka aka kulla.

Ana sa bangaren Shugaba Ilham Aliyev na kasar Azerbaijan ya bayyana imanin za a kawo karshen rikicin wanda aka shafe kimanin wata guda ana musanyen wuta tsakanin bangarorin biyu, amma ya yi gargadin cewa sojoji za su ci gaba da zama cikin shiri idan kasar Armeniya dauki wani matakin da ya saba za su mayar da martani.

 

News Source:  DW (dw.com)