Takun saka tsakanin Najeriya da Twitter

Takun saka tsakanin Najeriya da Twitter
Gwamnatin Najeriya ta bayyana matakin rufe kafar sada zumunta na Twitter har abinda hali yayi, kwanaki kadan bayan da kamfanin ya janye wani sako da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya wallafa.

A cikin wata sanarwar da ma'aikatar yada labarun kasar ta fitar a wannan Jumma'a, gwammnatin ta ce matakin zai ci gaba da aiki har sai abinda hali yayi, bisa zargin kamfanin da nuna wasu halayya ciki har da na nuna goyoyn baya ga masu zanga-zangar EndSARS da ta barke a kasar a baya.

Ministan yada labaran Najeriya Lai Muhammed yace idan kamfanin Twitter yana da nasa ka'idodi, to haka shi ma shugaban Najeriya yana da hurumin yin tsokaci kan halin da ake ciki.

A ranar Larabar da ta gabata ce kamfanin ya rufe shafin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bisa zargin keta ka'iddojinsa bayan shugaban kasar ya wallafa wani sako.

A daya gefen shima kamfanin sada zumunta na Facebook, ya bayyana makain soke shafin tsohon shugaban Amirka Donald Trump har na tsawon shekaru biyu, bisa abinda ya kira taka ka'idodin shafin.

News Source:  DW (dw.com)