Taliban: Ba mu san da zaman al-Zawahri ba

Taliban: Ba mu san da zaman al-Zawahri ba
Kungiyar Taliban ta ce tana gudanar da bincike kan kisan da Amirka ta yi ikirarin yi wa Shugaban kungiyar al-Qaida Ayman al-Zawahri a wani harin jiragen yaki marar matuki a babban birnin kasar Afganistan wato Kabul.

Sai dai kungiyar ta dage a cikin wata sanarwa cewa ba ta da masaniya kan shigowa da kuma mazaunin al-Zawahri a Afghanistan, sanarwar ta kasance karo na farko da kungiyar ta Taliban ta yi jawabi tun bayan harin da Amitka ta ce ta kai a ranar Lahadi.

Kisan al-Zawahri ya kara dagula dangantaka tsakanin Taliban da kasashen Yamma, musamman yayin da Taliban din ke  neman agajin gaggawa na kudin gudanar da sabuwar gwamnatinsu da ke fuskantar matsalar tattalin arziki tun bayan kwace mulki daga gwamnatin fara hula a bara.

News Source:  DW (dw.com)