Taliban za ta sayi mai daga Rasha

Taliban za ta sayi mai daga Rasha
Gwamnatin Taliban na kan mataki na karshe na tattaunawa a birnin Moscow, kan batun kwangilar sayen man fetur da gas daga kasar Rasha.

Habiburahman Habib, kakakin ma'aikatar tattalin arzikin kasar Afghanistan ya tabbatar da cewa wata tawaga a hukumance karkashin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan ta je babban birnin kasar Rasha inda ta kammala kwangilar samar da alkama, gas da mai.

Ya zuwa yanzu gwamnatin Moscow ba ta yi martani ba, amma wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amirka ke kokarin shawo kan sauran kasashen duniya da su daina amfani da man kasar Rasha, tana mai cewa shirin na da nufin dakile kudaden shigar man da Moscow ke amfani da shi wajen mamaye kasar Ukraine.

A halin da ake ciki dai kasashen Rasha da Afghanistan da Taliban ke jagoranta, na fuskantar takunkumin tattalin arziki daga gwamnatocin kasashen duniya ciki har da Amirka.

News Source:  DW (dw.com)