Taron yaukaka zumunta tsakanin Afirka da Turai

Taron yaukaka zumunta tsakanin Afirka da Turai
An gudanar da taro kara dankon zumunta tsakanin kasashen tarayyar Turai da na nahiyar Afirka.

A karon farko a tarihin nahiyoyin, gwamnatoci da yan kasuwa da yan siyasa da kuma kungiyoyin fararen hula a nahiyoyin afirka da Turai sun gudanar da wani taro a birnin Barlin na kasar Jamus.

Taron ya maida hankali ne wajen yaukaka dakon zumunta da habbaka tattalin arzikin yankunan guda biyu da annobar Corona ta yi wa illa ta hanyar samar da ayyukan yi. Taron har ila yau ya yi wata doguwar tattaunawa kan batun annobar COVID-19 da ma rigakafinta.
 

News Source:  DW (dw.com)