Tekun Bahar Rum babbar makabarta ce - Paparoma Francis

Tekun Bahar Rum babbar makabarta ce - Paparoma Francis
Shugaban darikar Katolika na duniya ya ce dubban 'yan ci rani da 'yan gudun hijira na asarar raukansu a yunkurin tsallakawa ta ruwa shiga Turai samun rayuwa mai inganci.

Da yake magana a gaban mabiya a fadarsa da ke birnin Batikan, Paparoma ya bukaci kasashen duniya da su kai agajin gaggawa ga dubban fararen hula ga mabukata a yankin Tigray wandanda yaki ya dai-daita a kasar Habasha,

Wannan ba shi ne karon farko da Paparoma Francis yake tsokaci a kan batutuwan da suka shafi rayuwar 'yan gudun hijira ba. Yanzu haka dai 'yan gudun hijira sama da 670 suka rigamu gidan gaskiya a tekun Bahar Rum a 2021 a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

News Source:  DW (dw.com)