Trump da Biden sun yi muhawarar karshe

Trump da Biden sun yi muhawarar karshe
A Amirka an gudanar da muhawara ta karshe a tsakanin shugaban kasa Donald Trump na jami'iyyar Repulican da kuma abokin hammayarsa Joe Biden na jamiyar Demockrat kwanaki 11 kafin zabe.

A muhawarar Joe Biden ya dora alhakin asarar rayukan da aka samu a game da cutar coronavirus da kakausar suka kacokam a kan shugaba Trump a wani abin da ya kira sakaci da rayukan alumma, ya kuma ce bai kamata ya sake komawa wannan kujera ta shuigabancin Amirka ba.

A daya bangare Donald Trump ya caccaki abokin hamayar sa ne da cewar zai boye a karkashin inuwar dokar Corona ya lalata tattalin arzikin kasar.

Rahotanni dai sun nuna cewar a wannan karon muhawarar ta gudana ne cikin natsuwa ba kamar a lokacin baya ba.
 

News Source:  DW (dw.com)