Tsohuwar shugabar Myammar Aung San Suu Kyi za ta gurfana a gaban kuliya a yau

Tsohuwar shugabar Myammar Aung San Suu Kyi za ta gurfana a gaban kuliya a yau
A wannan Talata ce tsohuwar shugabar gwamnatin kasar Myanmar Aung San Suu Kyi za ta gurfana a gaban kuliya, rana guda bayan kin zuwa kotun da ta yi.

Suu Kyi mai shekaru 76 da ke fuskantar tuhume-tuhume tun bayan da sojin kasar suka kifar da gwamnatinta a farkon watan Fabarairun shekarar nan, lauyoyinta sun ce ba ta iya gurfana a gaban kotu ba a sabili da jiri da take fama da shi.

Lauyoyinsun kara da cewar hakan na zuwa ne bayan yar gajeruwar tafiyar da aka yi da ita daga inda ake ci gaba da tsare ta zuwa zauren kotu.

Kasar ta Myammar dai ta kasance a cikin wani hali na rashin tabbas tun bayan da sojoji suka karbe madafun iko, ya zuwa yanzu sama da mutum dari biyar ne suka rasa rayukansu, lamarin da Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin shawo kan matsalar kafin ya kai ga rincabewa.
 

News Source:  DW (dw.com)