Ukraine ta kama hanyar shiga EU

Ukraine ta kama hanyar shiga EU
Mambobi a Kungiyar Tarayyar Turai sun shiga zaman taron amincewa da bukatar kasar Ukraine ta zama mamba a cikin kungiyar mai mambobi 28.

Kungiyar Tarayyar Turai da yanzu haka keda mambobi ashirin da takwas, za ta yi wani zama a birnin Brussel na kasar Beljiyam don tattauna yiyuwar amsar kasashen Ukraine da Moldova a matsayin mambobi a cikin kungiyar. Ukraine na fatan ganin ta samu sahalewar EU ta la'akari da barazanar da ta ke fuskanta daga Rasha da ta kaddamar da yaki a kanta. Wannan zai kasance matakin farko daga cikin matakan da ake bukata kafin zama cikakken mamba a kungiyar.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gabanin zaman taron, shugaban majalisar EU Charles Michel ya ce, kungiyar na fuskantar wani yanayi mai cike da sarkakiya amma hakan ba zai hanata nazari don cimma matsaya kan tsaro da daidaiton al'amura a yankin da ke fuskantar tarin kalubale musanman batun makamashi da akasarin kasashen Turai ke dogaro da Rasha a yayin da Mosko ke ci gaba da mamayar makwabciyarta Ukraine.
 

News Source:  DW (dw.com)