Wani hari ya salwantar da rayuka a Kamaru

Wani hari ya salwantar da rayuka a Kamaru
Wani sabon hari da 'yan bindiga suka kaddamar a kudancin kasar Kamaru, ya yi sanadiyyar salwantar rayuka wasu mazauna kauye da ke a iyakar kasar da tarayyar Najeriya.

Akalla mutum 26 ne aka tabbatar da cewa sun salwanta a wani hari da aka kai wa lardin Akwaya da ke a yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru a karshen  mako.

Rahotannin da ke fitowa daga yankin wanda ya yi kauren suna da miyagun ayyukan masu ikiraren ballewa daga Kamarun, na cewa harin na ranar Asabar ya ta'azzara lamura a tsakanin wadanda da ma ke fama da fitintinu na kabilanci da ma na ikon mallakar filaye.

Tun a shekara ta 2017 ne dai 'yan bindiga a yankin renon Ingila na Kamaru, suka kunna wutar rikici da gwamnatin Shugaba Paul Biya, saboda zargin maida su saniyar ware a kasar.

Sabon harin dai ya shafi mazauna kauyen Ballin ne, yankin kuma da ke iyaka da Najeriya.

News Source:  DW (dw.com)