Yerima bin Salman na ziyara a Turkiyya

Yerima bin Salman na ziyara a Turkiyya
Yerima Mohammed bin Salman mai jiran gado, zai ziyarci Turkiyya a karon farko tun bayan cece-ku-ce kan kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santabul a 2018.

Ganawar Shugaba Raccip Tayyip Erdogan da bin Salamn, ana masa kallon wani yunkurin Saudiyya mai arzikin man fetir na farfado da darajar masarautar, yayin da a nashi bangaren Erdogan zai ci gajiyar neman kudi da huldar diflomasiyya don ceto tattalin arzikin kasar gabanin zaben badi.

Tattaunawar da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman da Shugaba da Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya na zuwa ne wata guda kafin shugaban Amirka Joe Biden ya kai ziyara birnin Riyadh domin halartar taron yankin da ya mayar da hankali kan tabarbarewar makamashi sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

Gwamnatin Erdogan mai tushe ta addinin Islama ta fitar da wasu munanan bayanai game da kisan da suka hada da zargin cewa gawar Khashoggi ta lalace tare da narkar da sassanta da sinadarai. Sai dai a yanzu haka tana yin kaca-kaca da zuba jari da taimakon babban bankin kasar daga kasashen da ta ke adawa da su bisa dalilai na akida bayan boren kasashen Larabawa.

"Ina ganin watakila wannan ita ce ziyara mafi muhimmanci da wani shugaban kasar waje ya kai birnin Ankara cikin kusan shekaru goma,"in ji wani mai sharhi a Turkiyya Soner Cagaptay. Shugaban na Turkiyya zai tarbi yarima mai jiran gado a fadarsa, sannan kuma ya karbi bakuncinsa a wani liyafar cin abinci na sirri.

Ba a shirya taron manema labarai ko bikin sanya hannu ba yayin ganawar tasu. Manazarta na ganin yarima Mohammed zai yi kokarin ganin ko zai iya samun karin goyon baya gabanin sabuwar yarjejeniyar nukiliyar da za a yi tsakanin manyan kasashen duniya da kuma babbar kishiyar Saudiyyar wato Iran. "Akwai ƙarin tabbaci a Riyadh cewa gwamnatin Ankara na iya amfana ta fuskar siyasar yanzu,"in ji binciken kungiyar Eurasia.

Tuntubar juna tsakanin Turkiyya da Saudiya ta fara ne da hukuncin da wata kotu a Santanbul ta yanke a watan Afrilun shekarar 2022 na soke shari'ar da ake tuhumar mutane 26 da ake zargi da alaka da kisan Khashoggi tare da mayar da shari'ar zuwa Riyadh. Jami'an leken asirin Amirka sun tabbatar da cewa Yarima Mohammed ya amince da shirin na Khashoggi wanda Riyadh ta musanta.

News Source:  DW (dw.com)