Yunkurin sasanta rikicin Rasha da Ukraine

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da cewa yana sa ran ganawa da takwaransa na kasar Chaina Xi Jinping wanda ke zama daya daga cikin manyan abokan Poutine.

Wannan na zuwa ne bayan da Chaina ta wallafa wani kundi mai dauke da shafuka 12 a game da batun sasanta rikicin da Rasha da Ukraine ke yi cikin rawan sanhi a yayin da aka cika shekara guda da fara yaki tsakanin kasashen biyu.

A hirarsa da manema labarai Zalensky ya karkafa fatan ganin cewa Chaina ba za ta aike wa Rasha da makamai ba kamar yadda Amurka ke zarginta da yi.

Kasashen Yamma sun yi fatali da shawarwarun da ke kunshe a cikin kundin da ma'aikatar harkokin wajen Chaina ta wallafa a ranar 24 ga watan Fabarairu to sai dai shugaba Zalensky na Ukraine ya jaddada mahinmanci gudumuwar da Chainar ka iya bayar wa wajen kawo kashen mamayar da Rasha ke yi wa kasarsa.

News Source:  DW (dw.com)