Yunkurin tabbatar da doka a Amirka

Yunkurin tabbatar da doka a Amirka
Jami'an tsaro a Amirka dauke da bindigogi sun fara sintiri kan manyan titunan birnin Washington, a wani mataki na zaman cikin shirin ko takwana a gabani da ranar rantsar da zababben shugaban Amirka Joe Biden.

Shedun gani da ido sun tabbatar da ganin jami'an tsaron dauke da bindigogi, duk da yake majiyar tsaron kasar ta ki ta tabbatar da hakan ga manema labarai, tana mai cewa kawai sintirin jami'an tsaro a Washington, a wani mataki na ba wa 'yan sanda gagarumin dauki na ganin sun tabbatar da doka da oda.

Masu sharhi sun bayana cewa, 'yan jagaliyar siyasar da ke goyon bayan Donald Trump, sun yi sha alwashin barazanar fitowa domin tayar da hatsaniya a ranar bikin rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban kasa, lamarin da ya kai ga ma'aikatar tsaro ta Pentagone daukar matakin baza akalla jami'an tsaro 15000 a binrin.

News Source:  DW (dw.com)