Za a janye Barkhane daga Sahel

Za a janye Barkhane daga Sahel
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da cewar za a kawo karshen aikin rundunar tsaro ta Barkhane ta hanyar rundunonin tsaro na Faransa da ke yaki da ta'addanci a Sahel.

Ko da yake shugaban na Faransa ya ce za su janye daga aikin na yaki da ta'addanci a cikin rundunar, amma ya ce sojojin su za su ci gaba da aiki a cikin rundunar soji ta hadin gwiwa tsakanin Turai da kasashen Afirka Takuba domin yakin da ta'addanci. Faransa na da sojoji sama da dubu biyar a cikin rundunar ta Barkhane da aka kafa tun a shekara ta 2014 wacce ta yi nasara kwato yankin arewacin Mali da kungiyar 'yan ta'adda ta Abzinawa ta kwaci iko da shi tun 2012. Fransa ta yanke shawarar dakatar da ayyukan sojojin ta ne a Mali bayan juyin mulki da sojojin suka yi na kiffar da gwamnatin wucin gadi ta farar hula a makonnin da suka gabata.
 

News Source:  DW (dw.com)