Za a soma rigakafin cutar coronavirus a Jamus

Za a soma rigakafin cutar coronavirus a Jamus
Bayan da ta soma shan suka kan jinkiri wajen soma rigakafin annobar corona, ma'aikatar lafiyar Jamus ta tabbatar da soma amfani da rigakafin cutar corona a dukkanin sassan kasar.

A yayin wani jawabinsa a gaban majalisar dokoki ta Bundestag, ministan kiwon lafiyar Jamus Jens Spahn, ya bayyana cewa hukumomin Jamus na sa ran kammala alluran riga kafin corona akalla miliyan 13 cikin tsukin watanni uku. Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da cibiyar kula da yaduwar cututukan Jamus ta Robert Koch, ta tabbatar da samun mutuwar mutane 19 600 sabbin kamuwa da cutar corona a cikin kwana guda, a yayin da wasu fiye da mutun dubu daya suka rigamu gidan gaskiya.

News Source:  DW (dw.com)