Zanga-zanga a birnin Kandahar

Zanga-zanga a birnin Kandahar
Dangi da 'yan uwan iyallan sojojin tsohuwar gwamnatin Afghanistan sun yxi zanga-zanga a birnin Kandahar kan nuna kin amincewa da matakin gwamnati na fitar da su daga sansanin sojojin da suka samun mafaka.

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Kandahar da ke kudancin Afghanistan, a ci gaba da nuna rashin jin dadi kan matakin sabbin mahukuntan kasar na cewa su fice daga sansanin sojan yankin da suke samun mafaka.

An gudanar da zanga-zangar ne a harabar ofishin gwamnan Kandahar din, kana kuma wasu hotunan bidiyo sun nuna yadda masu boren suka toshe manyan hanyoyi a birnin.

Har yanzu da akwai mutane akalla dubu uku da suka ha da dangi da iyalan sojan tsohuwar gwamnatin Afghanistan da ke ci gaba da zama a sansanonin sojan na Kandahar, inda rahotanni ke cewa kungiyar Taliban ta ba su wa'adin kwanaki uku kacal dan su fice daga sansanin. Sai dai kawo yanzu kungiyar ta ba kara cewa uffan kan wannan batun ba.

News Source:  DW (dw.com)