Ambaliyar ruwa ta raba dubunnan mutane da matsugunansu a Itopiya

Ambaliyar ruwa ta raba dubunnan mutane da matsugunansu a Itopiya

Mutane sama da dubu 32 ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a jihar Afar da ke arewa maso-gabashin Itopiya.

Sanarwar da aka fitar daga Ofishin Yaki da Annoba da Samar da Abinci na jihar Afar ta ce bayan cika da kogin Awash ya yi ne ruwa ya balle tare da barnatar da amfanin gona da dabbobi.

Sanarwar ta ce mutanen da ke kewaye da kogin na bukatar taimakon abinci cikin gaggawa, wasu kauyukan yankin sun cika makil da ruwa yayinwa karin mutane dubu 63 ke fuskantar barazanar rasa matsugunansu.

News Source:   ()