An bayar da sabuwar sanarwar Navtex saboda Oruc Reis

An bayar da sabuwar sanarwar Navtex saboda Oruc Reis

Turkiyya ta fitar da sabuwar sanarwar Navtex saboda jirgin ruwan binciken albarkatun man fetur da iskar gas na Oruc Reis da ke aiki a Gabashin Bahar Rum.

Jirgin ruwan na Oruc Reis zai gudanar da aiyuka a kudancin Tsibirin Meis a ranar 22 ga Oktoba har zuwa karfe 21.00 agogon Turkiyya.

Jirgin ruwan Oruc Reis tare da jiragen ruwa 'yan rakiya na Ataman da Cengizhan za su gudanar da aiyukan neman albarkatun iskar gas a a Gabashin Bahar Rum.

Jirgin da aka samar da kaso 90 dinsa a cikin gida Turkiyya, na da tsayin mita 87 da fadin mita 23. Jirgin na da karfi da ikon gudanar da dukkan wani nau'i na binciken albarkatun ruwa.

 

 

News Source:   ()