An budewa masu masu zanga-zanga wuta a Iraki

An budewa masu masu zanga-zanga wuta a Iraki

Mutane 4 sun samu raunuka sakamakon bude wuta da jami'an tsaron Iraki suka yi kan masu zanga-zangar nuna bacin rai ga yawan katsewar lantarki da ake samu a jihar Wasit ta kudancin kasar.

Daruruwan mutane da ke son yin zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu ga yawan katsewar hasken lantarki sun taru a gaban cibiyar rarraba lantarki ta Al-Aziziyya.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, an jikkata mutane 4 wadanda 3 daga ciki suke cikin mawuyacin hali, an kuma kai wadanda suka jikkatan zuwa asibiti.

Ministan Lantarki na Iraki Majid Mahdi Hantush ya yi murabus a makon da ya gabata saboda yawaitar zanga-zangar adawa da yawan katsewar lantarki a kasar.

A kasar da darajar yanayi ta kai kusan 50 mutane na wahaltuwa a lokacin da aka dauke lantarki.

News Source:   ()