An dage lokacin harba tauraron dan adam na Turksat 5A

An dage lokacin harba tauraron dan adam na Turksat 5A

An dage aiyukan harba tauraron dan adam na Turkiyya na biyar mai suna Turksat 5A.

An dage harba tauraron na Turksat 5A da aka shirya harba shi zuwa sama a cibiyar harba makaman roka ta Cape Canaveral da ke jihar Florida ta Amurka.

Bayanan da TRT ta samu game da harba tauraron na cewar, an samu matsalar kauratar yanayi da kuma matsanancin gajimare a yankin.

Sakamakon haka aka dage harba tauraron dan adam din na Turkiyya na biyar.

Tauraron Turksat 5A zai yi aiyukan sadarwa a Turkiyya, Turai, Gabas ta Tsakiya, Arewacin Afirka, Tsakiyar Yammacin Afirka, Kudancin Afirka, Bahar Rum, Tekun Agean da Bahar Maliya.

News Source:   ()