An samu bunkasar fitar da kayayyaki a Turkiyya

An samu bunkasar fitar da kayayyaki a Turkiyya

Ministan harkokin kasuwancin kasar Turkiyya Ruhsar Pekcan ta bayyana cewa a shekarar 2020 kasar Turkiyya ta fitar da kayayyakin da ba ta taba irinsa ba a tarihi. 

Pekcan ta yi sharhi akan fitar da kayayyakin da kasar ta yi a cikin shekarar 2020.

Pekcan ta bayyana cewa a shekarar 2020 an yi nasarar fitar da kayayyaki da karin kaso 16 cikin dari na kudi dala biliyan 17 da miliyan 844 idan aka kwatanta da na shekarar 2019.

Ministan ta kara da cewa hakan na nuni ga karin samun nasarar fitar da kayayyakin daga kasar Turkiyya. 

A shekarar 2020 an fitar da kayayyaki da karuwar kaso 77.3 cikin dari, idan aka cire kayan ado na zinari a jumlace an fitar da kayayyakin da suka kai kaso 85.8 cikin dari. 

 

 

News Source:   ()