An samu bunkasar kanfuna a kasar Turkiyya

An samu bunkasar kanfuna a kasar Turkiyya

An sanar da cewa an kafa sabbin kanfanu dubu 10,603 a cikin watan Satumba a fadin kasar Turkiyya wanda ya nuna karin kaso 37.77 cikin dari.

A cikin lissafin wata- wata an samu karin kaso 13.38 cikin dari, kamar yadda Kungiyar Kasuwancin Kayyyakin Kasar ta TOBB ta bayyana.

An kuma bayyana cewa an rasmu rufe kanfuna 1,470 a fadin kasar wanda suka kai kaso 18.45 cikin dari.

Kaso 85 cikin darin kanfunan na mallakar day daikun mutane inda kaso 13 cikin darinsu kuwa suka kasasance nah adin gwiwa.

Jaridar Daily Sabah ta rawaito cewa, manyan sassa uku da kanfunan ke hidima a kansu su ne saye da sayarwa, kere-kere da gine -gine.

News Source:   ()