"Takunkumin Amurka ya sanya Iran hasarar dala biliyan 20"

"Takunkumin Amurka ya sanya Iran hasarar dala biliyan 20"

Shugaban babban bankin kasar Iran Abdunnasır Himmeti ya bayyana cewa sanadiyar takunkuman da Amurka ta kakkabawa kasarsa Iran ya sanya kasar yin hasarar kimanin dala biliyan 20 a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Himmeti, kamar yadda ya yada a kafarsa na Instagram ya bayyana cewa "Takunkumin da Amurka ta kakkabawa Iran babu irinsa"

A yayinda da Himmeti ke bayyana cewa Amurka ta kakkabawa dukkanin kanfunan Iran dake kasashen waje takunkumin ya kara da cewa,

"A cikin shekaru biyu da suka gabata, Iran ta samu kudade kasa da dala biliyan 20 kamar yadda ta saba samu, lamarin da ya sanya raguwar abinda babban bankin ke samu"

Himmeti ya kuma sanar da cewa kudaden shigar da kasar ke samu gabanin takunkuman ya kai dala biliyan 40 a fannin man kasar.

 

News Source:   ()