Azabaijan ta aika wasikar rashin amincewa ga Sberbank

Azabaijan ta aika wasikar rashin amincewa ga Sberbank

Babban Bankin Azabaijan (AMB) ya aika da wasikar nuna rashin amincewa ga Sberbank ta Rasha, wacce ta ba da damar bude asusu don taimaka wa abin da ake kira gwamnatin Armeniya na Nagorno-Karabakh, inda ta nemi a rufe asusun ba tare da bata lokaci ba.
A sanarwar da AMB ya fitar, an bayyana cewar an bude asusun taimako a Sberbank don abin da ake kira gudanarwar yankunan Azabaijan da aka mamaye. A sanarwar an bayyana cewar AMB, wanda ya aika da wasikar ya bukaci Sberbank da ya rufe wannan asusun nan take.
A wasikar an bayyana cewar a irin wannan lokaci mai matukar muhimmanci, shiga cikin aikin taimakawa tsarin mulki da ya saba doka zai lalata allakar Azabaijan da Rasha da kuma darajar banki mai tasiri kamar Sberbank.
A wasikar an kara da cewa duk wani aiki na tattalin arziki da ake gudanarwa a yankunan da aka mamaye ba tare da yardar Azabaijan ba ya saba wa dokokin kasa da kasa da na Azabaijan.

News Source:   ()