Bankin Duniya yayi magana game da tattalin arzikin Turkiyya

Bankin Duniya yayi magana game da tattalin arzikin Turkiyya

Bankin Duniya ya kiyasta cewa tattalin arzikin Turkiyya ya karu da kashi 0.5 cikin 100 a shekarar 2020.

Bankin Duniya ya buga alkaluman watan Janairun 2021 na Rahoton Tattalin Arzikin Duniya.

A cikin rahoton, an lura cewa an tsammani cewa tattalin arzikin duniya zai ragu da kashi 4.3 cikin 100 a shekarar 2020, kashi 4 cikin 2021 da kuma 3.8 a 2022 sakamakon sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19).

Rahoton ya bayyana cewar duk da hasashen raguwar tattalin arzikin kasashe da dama a shekarar 2020, karuwar tattalin arzikin kasashen Turkiyya, China, Masar da Bangladesh ya jawo hankalin duniya.

A cikin rahoton, an sanya tsammanin ci gaban tattalin arzikin Turkiyya a matsayin kashi 0.5 cikin 100 a shekarar 2020, kashi 4.5 a 2021 da kuma kashi 5 a 2022.

News Source:   ()