
Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wani bututun iskar gas a China.
Bayanan farko sun ce wasu mutane 8 sun jikkata sakamakon ibtila'in da ya afku a garin Dalian na jihar Liaoning na arewa maso-gabashin China.
Lamarin ya janyo firgici da dimuwa a yankin, kuma motoci da dama sun lalace.