Erdogan: Ana kai wa jirgin ruwanmu hari za mu mayar da martani

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewar ana kai wa jiragen ruwansu na fararen hula hari a Gabashin tekun Bahar Rum ba za su gajiya ba wajen mayar da martani nan take.

Bayan Sallar Juma'a a birnin ─▒stanbul, Shugaba Erdogan ya yi jawabi game da al'amuran da ke afkuwa a duniya a yau.

Erdogan ya ce idan har aka kuskura aka kai wa jirgin ruwansu na oruc Reis mai aiyukan neman albarkatun mai da iskar gas a Gabashin Tekun Bahar Rum hari, ba za su yi sanya ba wajen mayar da martani.

Ya ce "Oruc Reis zai ci gaba da aiyuka har nan da 23 ga Agusta. Mun tattauna kan wannan a ranar Alhamis din nan da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Ta ce tana bukatarmu da mu gudanar da wannan aiki cikin ruwan sanyi da tabbatar da bayar da kariya. Shugabar Jamus ta ce ta tattauna da Firaministan Girka Kiryakos Micotakis. Ina fata shi ma ta fada masa yadda ta fada mana."

Erdogan ya yi kira ga Micotakis da ya girmama dokokin kasa da kasa.

Ya ce "Sun kona kaburburan 'yan uwanmu da ke Yammacin Thrace. Wannan abu ne mai kyau ba. Mu ba za mu taba barin 'yan uwanmu da ke raye da wadanda suka mutu ba. Idan lokaci ya yi za mu yi abunda ya dace. Ina fadin wannan a bayyane."

 

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusgolu ya bayyana cewar ba Turkiyya ce ke janyo rikici a Gabashin Tekun Bahar Rum ba, Girka ce ke yin hakan.

Cavusoglu ya gudanar da taron manema labarai baya ganawa da takwaransa na Swizalan Ignazio Cassis.

Ya ce "Wutar rikici a Gabashin tekun Bahar Rum na daduwa. Amma ba Turkiyya ce ta ke janyo hakan ba, Girka ce."

Mu mun yi hakuri ba mu fara aiyukan neman albarkatun mai ba har zuwa shekarar 2018, amma Girka da Girkawan Cyprus sun fara wannan aiki sun kadai tun shekarun 2000.

Ya kuma kara da cewar suna yin aiki cikin nutsuwa da niya mai kyau sakamakon bukatar da Jamus da ke shugabantar Tarayyar Turai ta gabatar.

News Source:   ()