Erdogan: Istanbul na ci gaba da zama cibiyar hukumomin kasa da kasa

Erdogan: Istanbul na ci gaba da zama cibiyar hukumomin kasa da kasa

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewar, sun kara daukar wani mataki na mayar da birnin Istanbul cibiyar hukumomin kasa da kasa.

Shugaba Erdogan ya aike da sakon bidiyo zuwa ga taron bude ofishin Hukumar Hadin Kan Tattalin Arziki da Cigaba (OECD).

Erdogan ya ce, a aiyukan da za a gudanar a ofishin, yayi imanin OECD za ta samu gagarumar nasar.

Ya ce "Mun sake daukar wani mataki na ganin Istanbul ya zama Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomin kasa da kasa. Albarkacin ofishin OECD na Istanbul, za mu samu damar bayar da gudunmowa ga sauran sassan duniya a aiyukan da kungiyar ke yi."

Erdogan ya ce, OECD na gudanar da aiyukan yaki da annoba, tare da nemo bakin zaren warware matsalolin tattalin arziki da zamantakewa.

Ya ce "Cibiyar OECD da ke Istanbul za ta hada kai da helkwatar uwar kungiyar wajen hidimtawa mambobinta, sannan za ta habaka aiyukan hadin kan tattalin arziki da zuba jari da kasashen da ba mambobinta ba ne. Ina fatan wannan cibiya za ta dauki gudanar da manyan aiyuka. Muna fatan cibiyar Istanbul ta hanyar kulla sadarwa da Paris za ta gudanar da aiyuka sosai."

A jawabin da Ministar Kasuwanci ta Turkiyya Ruhsar Pekcan ta yi yayin halartar taron ta hanyar sadarwar bidiyo ta bayyana cewa, an bue sabon shafi a alakar Turkiyya da OECD.

Pekcan ta ce "Yanzu, lokaci ne sake gina duniya bayan annobar Corona. Muna sa ran wannan cibiya ta OECD da ke Istanbuyl za ta yi wannan aiki."

News Source:   ()