Erdogan: Turkiyya na tare da tsarin da zai tabbatar da adalci a Cyprus

Erdogan: Turkiyya na tare da tsarin da zai tabbatar da adalci a Cyprus

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewar, Turkiyya na tare a tsari na adalci da zai tabbatar da zaman lafiya da sulhu mai dorewa a Cyprus.

Bayan da Shugaba Erdogan ya gana da sabon zababben Shugaban Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus Ersin Tatar da ya kai ziyararsa ta farko a kasar waje zuwa Turkiyya, sun gudanar da taron manema labarai.

A jawabin da Shugaba Erdogan ya yi ya ce "Turkiyya na tare da tsari na adalci da zai samar da sulhu da zaman lafiya mai dorewa a Cyprus."

Da ya ke tabo halin da ake ciki a Gabashin Bahar Rum, Erdogan ya ce wadanda suke tayar da wutar rikicin su ne wadanda suka ki bin gargadin da aka dinga yi tun shekarar 2003 wato Girka da Cyprus Bangaren Girka.

Ya ce Cyprus Bangaren Girka sun ki daidaita kansu da Turkawa, sun ki yarda su yi aiki da kiran da  ake yi na a raba kudaden da ake samu daga albarkatun man fetur a yankin tare. Bangaren Girka da ke kallon Turkawa a matsayin marasa rinjaye, na ci gaba da danne hakkokinsu. A yanzu akwai mutane nau'i 2 a Tsibirin Cyprus da suka kafa kasashensu guda 2."

Shugaba Erdogan ya sake taya Ersin Tatar murnar zama Shugaban Kasa, kuma ya bukaci da ya gudanar da mulki bisa adalci da nuna kwarewa ta siyasa.

Erdogan ya ce zai ziyarci Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus a ranar 15 ga watan Nuwamba mai zuwa.

A nasa bayanin Ersin Tatar ya ce "Ba mu sanya idanu kan hakkin kowa ba, amma ba za mu taba bayar da dama wasu su cinye hakkin al'uamarmu ba."

News Source:   ()