Fitar da 'ya'yan itacen Rumman ya bunkasa a Turkiyya

Fitar da 'ya'yan itacen Rumman ya bunkasa a Turkiyya

Ķasar Turkiyya ta samu kudaden shiga har dala miliyan 98 daga fitar da 'ya 'yan itacen Rumman a shekarar 2019.

Kungiyar Tarayyar Ege ta fitar da alkaluman fitar da kayayyaki tsakanin watanin Janairu da Satumba wanda ya karu da zunzurutun kudi har kaso 37 cikin dari inda ya haura daga dala miliyan 43 da dubu 456 zuwa dala miliyan 59 da dubu 402.

Kasar Rasha ce ta sayi Rumman din miliyan 20 da dubu 243 wanda ya nuna karin 'ya 'yan itacen da take saye da karin kaso 78 cikin dari a cikin watanni 9.

A sahu na biyu kuma ķasar lraki ce wacce ke sayen na miliyan 12 da dubu 771 sai kuma Jamus mai sayen na miliyan 4 da dubu 870.

 

 

News Source:   ()