Fitar da ruwan zuma ya bunkasa a Turkiyya

Fitar da ruwan zuma ya bunkasa a Turkiyya

An sanar da samun bunkasar fitar da ruwan zuma daga kasar Turkiyya zuwa kasashe 45 inda aka siyar da ruwan zuman na dala miliyan 18 cikin watanni 9.

Hukumar Fitar da Kayayyaki ta Bahar Rum ce ta bayyana cewa tsakanin watanin Janairu zuwa Satumba an fitar da ton din ruwan zuma har dubu 4 da 101, inda aka samu kudaden shiga daga hakan har na dala miliyan 18 da dubu 196 da 233.

A bara a cikin wadanan watanin an fitar da ton dubu 3 da 556 na kudi dala miliyan 15 da dubu 672 da 422. Bisa ga haka a wannan shekarar an samu karin kaso 16 cikin dari idana aka kwatanta dana bara.

Kasashen Jamus, Amurka da Saudioyya ne suka siyar ruwan kudan zuman daga Turkiyya.

A shekarar da ta gabata kasashen Poland, Yemen, Bangladesh, Hungary, Djibouti, Denmark, Philippines, Switzerland, Panama, Cape Verde, Jamhuriyar Koriya ta Kudu da Guinea na daga cikin kasashe 45 da suka sayi ruwan kudan zuma daga kasar Turkiyya.

 

News Source:   ()