Mutane 5 sun mutu Indiya sakamakon zaftarewar kasa

Sakamakon zaftarewar kasar da mamakon ruwan sama ya janyo a Indiya, mutane 5 sun rasa rayukansu.

Sanarwar da mahukuntan Indiya suka fitar ta ce, a jihar Maharashtra da ke yammacin kasar sama da mutane dubu daya ake ci gaba a kokarin kubutarwa.

Nidhi Chaundhary da ke gudanar da aiyuka a yankin ya shaida cewa, sakamakon zaftarewar kasar da mamakon ruwan sama ya janyo mutane 5 sun mutu.

Chaudhary ya kara da cewa, ruwan sama da cikar da koguna suka yi sun ragu a yankin inda ake kuma ci gaba da aiyukan kubutar da wadanda ibtila'in ya shafa.

Rundunar sojin ruwan Indiya ta aika da jirgen sama masu saukar ungulu don kubutar da wadanda ibtila'İn ya rutsa da su.

News Source:   ()