Oruc Reis: Turkiyya ta mayarwa da Amurka martani

Oruc Reis: Turkiyya ta mayarwa da Amurka martani

Turkiyya ta mayar da martani ga Amurka dangane da jirgin ruwanta na Oruc Reis mai neman albarkatun iskar gas a tekun Bahar Rum.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya Hami Aksoy ya ce "Yadda Amurka ta soki aiyukan neman albarkatun mai da jirgin ruwan Oruc Reis ya ke yi a tekun Turkiyya abu ne na rashin kan gado."

Aksoy ya bayar da amsa a rubuce game da tambayar da aka yi kan kalaman kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Morgan Ortagus na sukar jirgin ruwan Oruc Reis da ke aiyukan neman albarkatun mai da iskar gas a Gabashin Bahar Rum.

Aksoy ya ce "Yadda Amurka ta soki aiyukan neman albarkatun mai da jirgin ruwan Oruc Reis ya ke yi a tekun Turkiyya abu ne na rashin kan gado."

Hami Aksoy ya bayyana irin rashin kan gadon Amurka da Tarayyar Turai da ke ikirarin cewar Taswirar Sevilla ba ta aiki a Gabashin Bahar Rum wadda ta ke nuna iyakokin Girka da Rumawa. Ya ce

"Ba Turkiyya ce ke tayar da zaune tsaye a tekunan Aegean da Bahar Rum ba, Kudancin Cyprus Bangaren Girka da Girka ne suke yin hakan."

News Source:   ()