Turkiyya da Yukiren zasu bunkasa cinikayya tsakaninsu

Turkiyya da Yukiren zasu bunkasa cinikayya tsakaninsu

Mataimakin ministan tattalin arzikin kasar Yukiren Taras Kaçka ya bayyana cewar kasarsa ta kara yin wata sabuwar yarjejeniyar cinikayya kai tsaye da kasar Turkiyya.

Kaçka ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Yukiren ta Ukrinform da cewa a yarjejeniyar cinikayya da ya dauki shekaru 7 ana gudanarwa an sake aminta akan muhimman abubuwan da ya kunsa tsakanin kasashen biyu.

Ya kara da cewa a watan Janairu kasashen biyu sun bayyana baiwa juna sabbin tayi wanda Yukiren ta karbi tayin Turkiyya a watan Agusta.

Muma a halin yanzu muna shirya namu tayin domin baiwa Turkiyya da hakan ne zamu sake zama mu tattauna da juna akan sabonta yarjeniyoyin cinikayya dake tsakaninmu

Bayan hakan kasashen biyu zasu sake zaman tattaunawa a watan Oktoba.

 

News Source:   ()