Turkiyya na ci gaba da taimakawa fararen hula a arewacin Siriya

Turkiyya na ci gaba da taimakawa fararen hula a arewacin Siriya

Turkiyya na ci gaba da bayar da taimako ga mata da yara kanana a gundumar Resul Ayn ta arewacin Siriya da aka kori 'yan ta'addar YPG/PKK daga cikinta.

Sashen Hidima da Kula da Kwamandojin Turkiyya ya raba takalman sanyi, rigunan sanyi da kayan abinci ga iyalai 12 da suka kunshi mutane 40 na Larabawa da Turkmen.

An rabawa yara marayu kuma kayan wasa.

A ranar 12 ga watan Oktoban 2019 ne aka fatattaki 'yan ta'adda daga gundumar Resul Ayn.

 

News Source:   ()