Turkiyya ta baiwa marayu taimako a Afganistan

Turkiyya ta baiwa marayu taimako a Afganistan

Kungiyar Bayar da Agaji ta Turkish Red Crescent ta bayar da taimako ga yara kanana marayu 247 da ke gidan kula da su na Alaattin a Afganistan.

Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta sanar da cewa,

"Dakarunmu da ke Afganistan, ta hannun Kungiyar Bayar da Agaji ta Turkish red Crescent sun bayar da taimako ga marayu 247. Kayan taimakon sun hada da kayan sawa, takalma, safuna da hulunan sanyi."

News Source:   ()