Turkiyya ta mayarwa da Girka martani game da Oruc Reis

Turkiyya ta mayarwa da Girka martani game da Oruc Reis

Turkiyya ta bayyana cewar jirgin ruwanta na Oruc Reis mai binciken albarkatun iskar gas na gudanar da aiyukansa a tekunta.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya Hami Aksoy ya fitar da rubutacciyar sanarwa game da tambayar da aka yi masa kan sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Girka ta fitar game da Oruc Reis da ke aiyuka a Gabashin Bahar Rum.

Aksoy ya ce, sanarwa mara tushe da asali Girka ta fitar inda ta ke cewar jirgin ruwan Turkiyya na Oruc Reis na neman albarkatun iskar gas a tekunsu, wannan kalami ne da ya sabawa doka da oda.

Ya ce, Oruc Reis na aiyuka ne a gabar ruwan Turkiyya da dokokin kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya suka ba ta. A ranar 23 ga Oktoba an sake yin karin haske ga Ofishin Jakadancin Girka da ke Ankara. A tsakanin 25 ga Oktoba da 3 ga Nuwamba, Oruc Reis zai gudanar da aiyuka a Gabashin Bahar Rum a nisan kilomita 440 daga Girka da nisan kilomita 130 daga Turkiyya.

Aksoy ya ci gaba da cewar Turkiyya a shirye ta ke a koyaushe ta yi zaman sulhu, kuma za ta ci gaba da kare hakkokinta da na Turkawan Arewacin Cyprus wadanda dokokin kasa da kasa suka ba su a Gabashin Bahar Rum.

Ya ce "Muna jiran Girka ta daina kame-kame game da kuran da muka yi mata na ta zo mu zauna a tattauna tare da nemo mafita."

News Source:   ()