Turkiyya ta taimakawa da iyalai dubu daya da kayan abinci a Sudan ta Kudu

Turkiyya ta taimakawa da iyalai dubu daya da kayan abinci a Sudan ta Kudu

A cikin watan Ramadhan mai alfarma da ya gabata, Turkiyya ta bayar da kayan taimako na abinci mai yawan tan 28 ga iyalai dubu 1,000 a Juba Babban Birnin Sudan ta Kudu.

Hukumar Hadin Kai da Cigaba ta Turkiyya (TIKA) ta fitar da rubutacciyar sanarwar cewa annobar Corona (Covid-19) ta sake jefa kasar Sudan ta Kudu da ke fama da talauci cikin mawuyacin hali.

Sanarwar ta ce TIKA ta bayar da kayan taimako na abinci mai yawan tan 28 ga iyalai dubu 1,000 a Juba Babban Birnin Sudan ta Kudu.

News Source:  www.trt.net.tr