Turkiyya ta taimakawa wadnada ambaliyar ruwa ta tagayyara a Sudan

Turkiyya ta taimakawa wadnada ambaliyar ruwa ta tagayyara a Sudan

Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent da ke Turkiyya ta bayar da kayan taimako ga iyalan da ambaliyar ruwa ta tagayyara a Sudan.

Kungiyar tare da hadin kan reshenta da ke Sudan sun raba kayan taimako ga iyalai 300 da ke gundumar Haşfaya da ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo ta tagayyara.

Wakilin tawagar Turkish Red Crescent a Sudan Serdar Yilmaz ya bayyana cewar sun raba kayan taimako a kwalaye dubu sama da 2 a gundumar Halfaya.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Sudan ta bayyana cewar mutane 138 sun rasa rayukansu a kasar sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku wadda mamakon ruwan sama ya janyo.

Sama da gidaje dubu 100 sun lalace ko rugujewa gaba daya, mutane 56 kuma sun jikkata.

Gwamnatin Sudan a ranar 5 ga Satumba ta aiyana dokar ta baci ta atanni 3 a kasar.

News Source:   ()