Yunwa na barazana ga rayuwar yara kanana dubu 98 a Yaman

Yunwa na barazana ga rayuwar yara kanana dubu 98 a Yaman

An bayyana cewar yunwa na barazana ga rayuwar yara kanana dubu 98 a kudancin Yaman.

Kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da ke Yaman sun bayyana cewar idan ba a dauki matakan yin magani ga yara kanana 'yan kasa da shekaru 5 da yunwa ke addaba ba, to za a rasa rayuka har dubu 98.

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) sun fitar da sanarwa ta hadin gwiwa da ke cewa

"Binciken karhe na Hukumomin 3 game da matsanancin rashin wadatacciyar cimaka, yara kanana dubu 98 na iya mutuwa a 2020, kuma an samu karin akso 10 na yaran da yunwa ke damu."

Binciken ya kuma bayyana cewar akwai yara kansa da shekaru 5 su miliyan 1,4 kuma lamarin ya shafi gundumomi 133.

Sanarwar ta ce "Akwai yara sama da rabin miliyan a kudancin Yaman a ke fama da karancin cimaka."

Sanarwar ta kuma ce matukar ba a yi magani ga yaran ba, to a wannan shekarar ta 2020 kimanin yara kanana dubu 98 na iya mutuwa a kudancin kasar da yaki ya daidaita.

News Source:   ()