A ranar Laraba za a yi bukin karbar Ozil zuwa Fenerbahce

A ranar Laraba za a yi bukin karbar Ozil zuwa Fenerbahce

A ranar Laraba 27 ga Janairu za a gudanar da bukin karbar dan wasan kwallon kafa Mezut Ozil zuwa kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya daga kungiyar Arsenal ta Ingila.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce, za a gudanar da buki a hukumance don sanya hannu da Mesut Ozil a cibiyar Divan Fenerbahce da ke Istanbul da misalin karfe 15.00 na ranar Laraba.

 

News Source:   ()