An fara bincikar Shugaban FIFA

An fara bincikar Shugaban FIFA

A kasar Swizalan an fara gudanar da bincke kan Shugaban Tarayyar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) Gianni Infantino.

Mai Gabatar da Kara na musamman da aka dauka a Swizalan Stefan Keller zai gudanar da bincike tare da nazari kan alakar Shugaban FIFA Infantino da Mai Gabatar da Kara na Swizalan Michael Lauber.

A makon da ya gabata ne Lauber ya yi murabus daga aikinsa, wanda shi ne ya jagoranci binciken da aka fara yi wa FIFA kan cin hanci da rashawa a shekarar 2015.

A shekarar 2016 kuma Infantino ya hau kujerar Shugabancin FIFA bayan murabus din da Sepp Blatter ya yi bisa zargin sa da aiyukan cin hanci da rashawa.

News Source:   ()