
A yankin Merga Butan na lardin Hakkari da ke Turkiyya, an fara nishadantuwa a cibiyar wasannin dusar kankara karkashin matakan kaucewa kamuwa da cutar Corona (Covid-19).
An budewa masu wasannin zamiya da guje-guje a dusar kankara cibiyar, wadda aka kashe Lira miliyan 15 wajen samar da ita.
A cibiyar, tudun dusar kankarar da ta zuba ya kai santimita 50, kuma masu wasanni na cikin gida da na kasashen waje na gudanar da atisaye da samun horo a wajen.
Haka zalika 'yan yawon bude ido ma na tururuwa don nishadantuwa a wajen.