An soke gasar MotoGP da aka dage lokacinta a baya

An soke gasar MotoGP da aka dage lokacinta a baya

An soke gasar tseren babura ta MotoGP rukunin Italiya wanda a baya aka dage lokacin gudanarwa saboda annobar Corona (Covid-19).

Rukunin gaar ta MotoGP da aka shirya gudanarwa a Italiya ya samu cikas sakamakon annobar Corona. A baya an gudanar da gaar a kasashen Katar, Jamus, Holan, Finlan, Ingila da Ostireliya.

Sanarwar da aka fitar daga shafin yanar gizon Hukumar da ke shirya gasar ta ce an soke gasar da aka dage lokacinat na tsakanin 29 da 31 ga watan Mayu.

Haka zalika sakamakon  annobar an dage gaar MotoGP da aka shirya yi a kasashen Amurka, Ajantina, Spaniya da Faransa.

News Source:  www.trt.net.tr